Isa ga babban shafi

China ta baza sojojinta a matsayin martani kan ziyarar Pelosi a Taiwan

Taiwan ta yi watsi da duk wata barazana bayan da ta karbi bakwancin Shugabar Majalisar Dokokin Amurka Nancy Pelosi, a daidai lokacin da China wadda ta fusata ta fara gudanar da wani atisayen soji da zummar nuna bacin ranta kan ziyarar.

China dai na kallon ziyarar ta Pelosi a matsayin tsokana daga Amurka
China dai na kallon ziyarar ta Pelosi a matsayin tsokana daga Amurka © Taiwan Presidential Office via AP
Talla

A yammacin Talata ne dai, Pelosi ta isa tsibirin na Taiwan duk da barazanar da ta fito daga China wadda ke kallon tsibirin a matsayin  yankinta , yayin da take cewa, tana kallon wannan ziyarar a matsayin tsokana daga Amurka.

China dai ba ta yi jinkirin mayar da martani ba, inda nan take, ta sanar da fara wani atisayen soji wanda ta ce, ya zama dole ta gudanar a kusa da gabar tekun tsibirnin na Taiwan.

Ma’aikatar Harkokin Wajen China ta ce, kasar ce za ta kwan a ciki a dalilin wannan ziyarar, yayin da shugabar Taiwan Tsai-Ing-wen ke cewa, babu yadda tsibirin mai yawan al’umma miliyan 23 zai mika wuya haka kawai.

Shugabar ta kara da cewa, za su ci gaba da shata layi wajen bai wa tsarin demokradiyarsu kariya duk da barazanar sojin da suke fuskanta daga China.

China dai ta jima tana kokarin katange Taiwan daga taka rawa a duk wani al’amari da ya shafi kasashen duniya, sannan tana gaba da duk wata kasa da ke mu’amala da tsibirin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.