Isa ga babban shafi

A shirye muke mu yi yaki saboda Taiwan -China

China ta gudanar da sabon atisayen soji a zagayen tekun Taiwan, tana mai caccakar sabuwar ziyarar kwanaki biyu da ‘yan majalisar Amurka suka kai tsibirin.

China ta sake gudanar da sabon atisayen soji a zagayen tsibirin Taiwan
China ta sake gudanar da sabon atisayen soji a zagayen tsibirin Taiwan via REUTERS - EASTERN THEATRE COMMAND
Talla

Wannan na zuwa ne bayan ziyarar da shugabar Majalisar Wakilan Amurka Nancy Pelosi ta kai Taiwan, lamarin da ya fusata gwamnatin China wadda ke daukar tsibirin a matsayin wani yankinta.

Yanzu haka sabuwar ziyarar da wasu mambobi biyar na Majalisar Amurkar suka sake kaiwa Taiwan din, ta sa China sake furta zafafen kalamai, tana mai cewa, za ta yi damarar yaki akan wannan tsibiri.

Tawagar ‘yan majalisar ta Amurka karkashin jagorancin Sanata Ed Markey daga Massachusetts ta gana da shugabar Taiwan Tsai Ing-wen a wannan Litinin.

Bayanai na cewa, tawagar ta Amurka ta samu damar musayar ra’ayoyi da Taiwan kan wasu batutuwa masu yawa da suka shafi kasashen biyu.

Shugabar ta Taiwan ta shaida wa tawagar ta Amurka cewa, tana son ci gaba da ganin dorewar matsayin Taiwan a tsibirinta tare kuma da tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a yankin tekun India da Pacific.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.