Isa ga babban shafi

Amurka da Taiwan na gab da kulla yarjeniyoyin kasuwanci a hukumance

Amurka ta sanar da shirin fara tattaunawar cimma yarjejeniyar kasuwanci a hukumance tsakaninta da Taiwan, matakin da ke zuwa makwanni bayan ziyarar shugabar majalisar wakilan kasar Nancy Pelosi da ta haddasa rikici tsakanin yankin mai kwarya-kwarya ‘yanci da China.

Ziyarar Nancy Pelosi a Taiwan.
Ziyarar Nancy Pelosi a Taiwan. AP
Talla

Ma’aikatar kasuwancin Amurka a sanarwar da ta fitar ta ce nan bada jimawa ba za a faro kakkarfar tattaunawar wadda za ta kunshi hada-hadar kasuwanci da cinikayya da kuma musayar fasahar zamani.

Alaka tsakanin Amurka da China ta kare tsami tun bayan ziyarar ta Pelosi wadda ta kai ga katse wasu yarjeniyoyi da ke tsakanin kasashen biyu.

Sanarwar ta ruwaito shugabar sashen kasuwanci ta Amurka Sarah Bianchi na cewa za su kulla gagarumar yarjejeniya da za ta amfani dukkanin bangarorin biyu.

A cewarta dukkanin bangarorin biyu sun a aminta da daftarin da suka mikawa juna batun fara tattauna da kuma rattaba hannu kadai ya rage gabanin fara aikinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.