Isa ga babban shafi

Taiwan ta fara wani kakkarfan atisayen Soji cike da fargabar mamayar China

Taiwan ta fara wani kakkarfan atisayen Soji da makaman atilare yau talata a wani mataki da ta bayyana da bai wa kan ta cikakkiyar kariya daga barazana, dai dai lokacin da China ke ci gaba da girke tarin makamai da Sojoji a zagayen yankin mai kwarya-kwaryar 'yanci.

Atisayen Sojin Taiwan.
Atisayen Sojin Taiwan. AP - Lin Jian
Talla

Taiwan wadda yanzu haka ke cike da fargabar yiwuwar fuskantar mamaya daga China bayan hasashen haka daga wani babban jami'in diflomasiyyarta, ta bayyana cewa ta na cikin shirin ko ta kwana don tunkarar kowacce barazana ba tare da fargaba ba.

Matakin atisayen Sojin na Taiwan ya zo ne dai dai lokacin da China ta kammala na ta atisayen mafi girma na tsawon kwanaki don mayar da martani ga ziyarar da shugabar majalisar dokokin Amurka Nancy Pelosi, ta kai yankin da China ke kallo a matsayin mallakinta.

Ministan harkokin wajen Taiwan Joseph Wu ya shaidawa taron manema labarai a Taipei cewa manufar China shi ne durkusar da yankin tsawon lokaci kawai dai ta fake da ziyarar Pelosi ne don aiwatar da shirinta.

A bangare guda wata sanarwar ma’aikatar tsaron China yau talata, ta ce atisayen Sojinta zai ci gaba kama daga wanda ta ke gudanarwa a ruwa da kuma na sararin samaniya.

Da tsakaddaren jiya litinin wayewar yau talata ne, Sojin na Taiwan suka faro atisayen ko da ya ke sa’o’I kalilan da fara aka kammala a cewar Lou Woei-jye kakakin ma’aikatar tsaron kasar.

Lou ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an tsara atisayen tun da jimawa kuma bashi da alaka da wanda China ke gudanarwa.

An gad ai yadda Sojin na Taiwan suka rika harba makaman atilare daga gabar howitzer zuwa cikin ruwa, yayinda Lou ke bayyana cewa sai a ranar alhamis ne atisayen zai ci gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.