Isa ga babban shafi

Ba zamu bar Taiwan ta wahala a hannun China ba- Amurka

Shugabar Majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi ta yi ikirarin cewa kasar ba za ta bar yankin Taiwan ya wahala a hannun China ba duk da barazanar atisayen Sojin da Beijing din ta fara a zagayen yankin.

Shugabar Majalisar Wakilan Amurka Nancy Pelosi.
Shugabar Majalisar Wakilan Amurka Nancy Pelosi. © The Australian
Talla

Pelosi ta bayyana cewa yankin Taiwan na bukatar ‘yancin sakewa ba tare da tunanin wata fargaba daga China ba.

A cewar Pelosi Amurka za ta yi amfani da kowanne salo wajen ganin Taiwan ba ta kasance saniyar ware ba, ba kuma ta fuskanci cutarwa daga China ba.

Tuni yankin ya bayyana cewa ya shiryawa yaki da China duk da cewa basa fatan barkewar yakin.

Haka zalika zuwa yanzu kungiyar Tarayyar Turai da ta kasashe 7 mafiya karfin tattalin arziki suka yi tir da matakin Chinar na fara atisayen.

Shi ma sakataren wajen Amurkan Antony Blinken bayan taronsa da manyan jami’an diflomasiyyar nahiyar Asia ya bayyana martanin Chinar kan ziyarar Pelosi a matsayin wani lamari mai matukar tayar da hankali da kidimarwa.

A zantawarsa da manema labarai, Blinken ya ce matakin na China ba Taiwan kadai zai cutar ba har da kasashen makwabta, yana mai cewa Amurka na bukatar kwantar da hankula amma hakan baya nufin ta katse huldarta da Taiwan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.