Isa ga babban shafi

China ta fara atisayen Soji a zagayen Taiwan don gargadi kan ziyarar Pelosi

Sojojin kasar China sun fara atisaye mafi girma a yankin Taiwan, a wani mataki na nuna karfin tuwo kan muhimman hanyoyin jiragen ruwa na kasa da kasa, bayan ziyarar da shugabar majalisar dokokin Amurka Nancy Pelosi ta kai tsibirin.

Wasu jiragen Sojin China da ke shawagi a saman ruwan yankin Taiwan.
Wasu jiragen Sojin China da ke shawagi a saman ruwan yankin Taiwan. AFP - HECTOR RETAMAL
Talla

Pelosi ta bar Taiwan ne a ranar Laraba bayan ziyarar da ta bijirewa jerin barazanar da China ta rika yi, wanda ke kallon tsibirin mai cin gashin kansa a matsayin yankinta.

Pelosi wadda ta kasance mai mukami mafi girma daga Amurka da ta ziyarci Taiwan cikin shekaru 25, ta sha alwashin ba za su yi watsi da yankin da su ke dauka a matsayin mai muhimmanci ba wajen karfafa dimokaradiyya.

Wadannan kalamai ne suka kara fusata China, wadda ta yi alkawarin mayar da martani tsattsaura tare da sanar da fara atisayen soji a ‘iyakokin ruwan tsibirin na Taiwan.

Dakarun na China sun fara atisayen ne, da misalin karfe 12 na daren jiya laraba, ba kuma tare da bata lokaci ba suka fara gwajin harba manyan makamai, a wasu yankuna 6 da ke zagaye da tsibirin na Taiwan, masu nisan kilomita 20 kacal daga ainahin cikin gari, atisayen da ba zai kare ba sai a ranar lahadi mai zuwa.

Ma'aikatar tsaron Taiwan ta ce ta na sa ido sosai kan atisayen na sojojin China, kuma tsibirin a shirye yake don tunkarar yaki, amma ba za ta fara takalo shi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.