Isa ga babban shafi

Ziyarar Pelosi ta janyowa Taiwan fushin China ta fuskar kasuwanci

Kasar China ta dakatar da shigar da kayan marmari da kuma kifi daga Taiwan a yau Laraba, inda ta kara da daukar matakin dakatar da jigilar kasa ko kuma yashi zuwa tsibirin na Taiwan, sakamakon ziyarar da shugabar majalisar dokokin Amurka Nancy Pelosi ke yi a yankin, duk da barazanar mayar da martani da China ta rika yi.

Shugabar Majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi tare da sahugabar yankin Taiwan Tsai Ing-wen bayan ganawarsu a fadar gwamnati.
Shugabar Majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi tare da sahugabar yankin Taiwan Tsai Ing-wen bayan ganawarsu a fadar gwamnati. © Taiwan Presidential Office via AP
Talla

Hukumar Kwastam ta China ce ta sanar da matakin dakatar da shigar da kayan marmari dangin lemu da kuma kifi cikin kasar daga Taiwan bisa zargin maimaita gano amfani da magungunan kashe kwari fiye da kima kan nau’ikan abincin.

Ita kuwa Ma'aikatar Cinikin kasar ta Sin,  ta sanar da dakatar da kaiwa Tsibirin na Taiwan Yashi ko kasa ne daga ranar Laraba, karin bayani ba.

Wannan dai ba shi ne karon farko da China ke lafta takunkumi kan kayayyakin da Taiwan ke fitarwa ketare ba, domin a watan Maris na shekarar 2021, kasar ta Sin ta haramta shigo da abarba daga tsibirin bayan sanar da gano wasu kwari a tattare da abarbar, matakin da wasu ke kallo a matsayin na siyasa.

Ziyarar Pelosi ita ce irinta ta farko da wanni babban jami’i daga Amurka ya kai zuwa yankin na Taiwan cikin shekaru 25, kuma jim kadan bayan saukarta a yankin, Pelosin ta ce zaman lafiya ne ya kaita tsibirin ba neman tashin hankali ba, said ai hakan bai hana China fusata ba.

Da yammacin ranar Talata shugabar majalisar dokokin Amurka ta sauka a yankin Taiwan duk da gargadin da kasar Sin ta yi mata, wadda ke daukar tsibirin Taiwan a matsayin wani bangare na kasarta, tare da sa ran kwato shi wata rana, ko da kuwa da karfin tsiya ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.