Isa ga babban shafi

Rasha ba ta yi wa shugaban dakarun Wagner afuwa ba

Hukumomin Rasha na ci gaba da gudanar da bincike kan shugaban dakarun haya na Wagner bisa yunkurinsa na yi wa kasar tawaye duk da cewa, an cimma yarjejeniyar sasantawa da shi.

Shugaban dakarun Wagner tare da wasu makusantansa
Shugaban dakarun Wagner tare da wasu makusantansa AFP - HANDOUT
Talla

Kamfanonin dillacin labaran Rasha sun rawaito cewa, yanzu haka ana gudanar da binciken kan Yevgeny Prigozhin wanda ya shirya dakarunsa na Wagner da suka kama hanyar kutsawa cikin birnin Moscow, fadar shugaba Vladimir Putin, lamarin da ya janyo hankulan kasashen duniya da suka yi mamakin faruwan hakan.

A yammacin jiya Lahadi fadar Kremlin ta shugaba Putin ta ce, ta cimma wata matsaya da shugaban na Wagner kan cewa, za ta janye duk wasu tuhume-tuhume a kansa, amma ya fice daga kasar zuwa Belarus don neman mafaka.

Sai dai sabbin bayanan da suka bulla a wannan Litinin sun nuna cewa, gwamnatin Rasha ba ta yi masa afuwa ba, tana mai cewa, ba a janye tuhumar laifukan da ake yi masa ba kamar yadda kamfanonin dillancin labaran kasar suka rawaito daga majiyar ofishin mai shigar da kara na gwamnatin kasar.

A yau Litinin rahotanni na cewa, birnin Moscow na kokarin ci gaba da hada-hadarsa ta yau da kullum kamar yadda aka saba bayan boren da wadannan sojojin na Wagner suka yi a karshen mako, wanda ya tilasta girke sojojin da suka yi damarar yaki a babban birnin.

Ministan Tsaron Rasha, Sergei Shoigu ya bayyana cewa, akwai wani faifain bidiyo da aka nada da ke nuna shugaban na Wagner ya ziyartar dakarun Ukraine, kasar da ke gwabza yaki da Rashar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.