Isa ga babban shafi

Al'ummar Isra'ila sun sake tsunduma zanga-zangar adawa da kudirin Netanyahu

Dubunnan al’ummar Isra’ila sun sake fantsama kan titunan manyan biranen kasar don kalubalantar kudirin Firaminista Benjamin Netanyahu na garambawul ga bangaren shari’a, kudirin da tuni ya haddasa rarrabuwar kan al’ummar kasar.

Wasu 'yan Isra'ila da ke zanga-zangar kin jinin kudirin garambawul ga dokar shari'a.
Wasu 'yan Isra'ila da ke zanga-zangar kin jinin kudirin garambawul ga dokar shari'a. AP - Ohad Zwigenberg
Talla

Dokar wadda bayanai ke cewa tuni Majalisa ta amince da ita duk da boren jama’a, yau talata anga yadda al’ummar Isra’ila suka yi fitar dango a biranen Jerusalem da Haifa da kuma Tel Aviv .

Zanga-zangar ta sake tsananta a yau ne sakamakon matakin majalisar kasar na yiwa kudirin dokar amincewar wucin gadi wanda zai bayar da damar kwace karfin ikon bangaren shari’a tare da mayar da shi ga mukarraban gwamnatin ta Isra’ila.

Bangaren adawar kasar wanda ya jima yana sukar wannan kudiri, ya kira matakin Majalisar da wani yunkurin na mayar da mulkin kasar na kama karya.

Wannan kudiri dai guda ne cikin tarin kudire-kudire da Netamyahu ya gabatar gaban Majalisar Wanda kuma ke san suka daga ‘yan kasar.

Bangaren ‘yan fafutukar da suka kira zanga-zangar ta yau, sun yi dafifi a muhimman wurare ta yadda suka hana hada hada hatta a babban filin jirgin saman kasar, ko da yake an jibge jami’an tsaro don kaucewa fuskantar rikici.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.