Isa ga babban shafi

Ana ci gaba da bore kan tsarin yiwa dokokin shari’a garambawul a Isra'ila

Masu zanga-zanga a Isra’ila sun sake gudanar da wata a jiya Asabar don nuna adawa da shirin firaminista Benjamin Netanyahu, na yiwa dokokin shari’a garambawul, kwanaki kadan bayan da ya ce ya janye wani kudiri daga ciki wanda ya janyo cece-kuce.

Yadda 'yan Isra’ila suka taro a babban birnin kasar Tel Aviv, don nuna adawa da shirin firaminista Benjamin Netanyahu na yiwa dokokin shari’a garambawul.
Yadda 'yan Isra’ila suka taro a babban birnin kasar Tel Aviv, don nuna adawa da shirin firaminista Benjamin Netanyahu na yiwa dokokin shari’a garambawul. REUTERS - OREN ALON
Talla

Masu zanga-zangar sun ci gaba da gudanar da zanga-zangar mako-mako don adawa da Netanyahu, wanda ya sake koma kan karagar mulki a watan Disambar da ya gabata, a karkashin wani kawancen  jam’iyun yahudawa masu tsattsauran ra'ayi da kuma masu ra'ayin mazan jiya.

Kamar yadda suka saba yi duk ranar Asabar tsawon watanni, masu zanga-zangar sun yi dafifi a tsakiyar babban birnin kasar Tel Aviv don nuna adawa da sauye-sauyen da gwamnati ta yi wa bangaren shari'a.

Masu adawa da sauyin na ganin cewa zai iya bude hanyar samun gwamnatin kama karya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.