Isa ga babban shafi

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump na fuskantar sabbin tuhume-tuhume

Tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump na fuskantar sabbin tuhume-tuhume bisa zargin yunkurin kawo cikas ga binciken badakalar wasu manyan bayanan sirri ta hanyar hada baki da goge faifan bidiyo a gidansa da ke Mar-a-Lago da ke Florida.

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump kenan, yayin wani yakin neman zabe a Bluffs, Iowa, ranar 7, ga Yulin 2023.
Tsohon shugaban Amurka Donald Trump kenan, yayin wani yakin neman zabe a Bluffs, Iowa, ranar 7, ga Yulin 2023. REUTERS - SCOTT MORGAN
Talla

Masu shigar da kara na gwamnatin tarayya sun bankado sabuwar tuhumar da ake yi wa mutumin da ke kan gaba a zaben fidda gwani na jam’iyyar Republican, wanda ake shirin gurfanar da shi a gaban kotu yayin da ake Shirin gudanar da babban zaben kasar a watan Mayun 2024.

Sabbin tuhume-tuhumen dai sun zo ne a ranar da Trump ya ce lauyoyinsa sun gana da jami’an ma’aikatar shari’a gabanin wata tuhuma ta daban da kan kokarinsa na soke sakamakon zaben 2020.

An fara gurfanar da tsohon shugaban da aka tsige har sau biyu a watan da ya gabata, wanda ake zargi da yin barazana ga tsaron kasa ta hanyar rike manyan bayanan sirrin nukiliya da na tsaro bayan ya bar fadar White House.

Trump ya ajiye bayanan da suka hada da bayanai daga hukumar liken asiri ta kasar, CIA da Hukumar Tsaro ta Kasa a gidansa da ke Mar-a-Lago a Florida tare da dakile kokarin da hukuma ke yi na kwato su, a cewar gwamnatin Amurkan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.