Isa ga babban shafi

Rasha ta kaddamar da dokar toshe kadarorin kungiyoyin waje da ke fuskantar takunkumi

Shugaba Vladimir Putin ya sanya hannu kan wata doka da ta bai wa bankunan Rasha da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi damar toshe kadarorin kungiyoyi da daidaikun mutane na kasashen waje da aka sanya wa takunkumi.

Shugaban Rasha Vladmir Putin, lokacin da yake gabatar da jawabi a taron kasashen Afirka da Rasha.
Shugaban Rasha Vladmir Putin, lokacin da yake gabatar da jawabi a taron kasashen Afirka da Rasha. AP - Pavel Bednyakov
Talla

Dokar ta bai wa Moscow damar rufe asusun ajiyar kudade da kadarorin hukumomin shari'a da 'yan kasashen waje da kungiyoyi ke sarrafawa wadanda Rasha ta sanya abin da ta kira matakan kare tattalin arzikinta na musamman.

Har ila yau, dokar hana hada-hadar kudi da ake gudanarwa don moriyar baki da aka sanya wa takunkumi.

Daga cikin jerin kamfanonin da abun ya shafa akwai, kantin sayar da kaya, masu ba da lamuni da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi da aka dakatar da yin ayyuka tare da baki da aka sanya wa takunkumi.

Babban bankin kasar Rasha ya ba da izini ya sanya takunkumin watanni shida kan wadannan cibiyoyin hada-hadar kudi idan aka same su da keta matakan tattalin arziki na musamman.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.