Isa ga babban shafi

China ta haramta amfani da halittun ruwa da suka fito daga Japan

Kasar Japan ta fara fitar da gurbataccen ruwan da aka tsaftace shi daga tashar nukiliyar Fukushima zuwa tekun Pasifik, lamarin da ya haifar da zanga-zanga a yankin, inda kasar China wadda ta kasance babbar mai sayen halittun ruwa ta ce za ta haramta shigar da su cikin kasarta. 

Masu rajin kare muhalli da ke zanga-zangar adawa da matakin Japan kenan.
Masu rajin kare muhalli da ke zanga-zangar adawa da matakin Japan kenan. © AP / Lee Jin-man
Talla

Japan ta ce ruwan tsarkakke ne, kuma masana kimiyya da dama sun yarda da amincinsa.

Ita ma hukumar kula da makamashin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da sahihancin ruwan. 

Sai dai masu suka sun ce akwai bukatar a kara yin nazari sannan a dakatar da fitar da ruwan har sai an gamsu da cikakkun bayanan da aka samu. 

Sama da tan miliyan daya na ruwan da aka adana a tashar nukiliyar za a kwashe cikin shekaru 30 masu zuwa. 

China wadda ta kasance cikin masu adawa da shirin tun bayan sanar da bukatar hakan shekaru biyu da suka gabata, ta bayyana matakin a matsayin son kai da rashin sanin ya kamata, ta kuma ce kasar Japan na ci gaba da gina wani mummunan rauni a kan al'ummomin da za su zo nan gaba. 

Ofishin hukumar shige da ficen kasar ta China ya sanar da cewa, za a tsawaita dokar hana shigo da halittun ruwa daga Fukushima da wasu larduna domin kare lafiyar jama'ar kasar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.