Isa ga babban shafi

Hare-haren Isra'ila sun kashe yara dubu 2 da 300 a Gaza - MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta koka kan yadda rikicin Isr’aila da Hamas ke ci gaba da lakume rayukan kananan yara a Gaza, tana mai cewa kawo yanzu hare-haren Isra’ila sun kashe yara fiye da 2,300. 

Palestinian children injured in an Israeli air strike await treatment at the Nasser hospital in Khan Yunis in the southern of Gaza Strip, on October 17, 2023.
Palestinian children injured in an Israeli air strike await treatment at the Nasser hospital in Khan Yunis in the southern of Gaza Strip, on October 17, 2023. AFP - MAHMUD HAMS
Talla

Kididdiga ta nuna cewa kawo yanzu yara dubu 2 da 360 ne suka mutu tun bayan tashin wannan rikici, kamar yadda UNICEF ta tabbatar, inda ta bukaci a gaggauta tsagaita wuta da kuma bada cikakkiyar dama ta aikin jin kai. 

Jawabin na UNICEF ya kuma ci gaba da cewa yara a Gaza dubu dubu 5 da 364 ne suka jikkata yayin da wasu karin 400 suka bata bat. 

UNICEF din ta kuma ce hare-haren da Isra’ila ke kaddamarwa na kashe rayukan yara kusan 400 kowacce rana a yankin da yara ne ke da yawan kaso 50 cikin 100 na mutane miliyan 2.3 da ke a Zirnin Gazan. 

Daraktar UNICEF da ke kula da Gabas ta Tsakiya da Arewacin Africa Adele Khodr ta ce wannan kashe-kashen yara a yankin na lalata tsarin Hukumar a Gabas ta Tsakiya da kuma nuna tsantsar rashin tausayi daga Isra’ila.  

Wannan yaki ya jefa kowanne yaro cikin tashin hankalin da kwakwalwarsu ba za ta iya dauka ba, yayin da wasu suka fada cikin cututtukan firgici da damuwa, baya ga yunwa, cututtuka da rashin ruwa da ke yi musu barazana a kowacce rana. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.