Isa ga babban shafi

Isra'ila ta baiwa Falasdinawa wa'adin sa'oi 4 su fice daga Gaza

Duniya – Kasar Isra’ila ta baiwa Falasdinawan dake Gaza da aka yiwa kawanye sa’oi 4 kacal da su fice daga yankin yau talata, ko kuma su gamu da fushin dakarun su, a daidai lokacin da wadanda ke barin wurin suka ce sun ga tankunan yakin da aka aje domin afkawa yankin.

Mashigin Rafah a yau Talata da Falasdinawa ke amfani da shi suna ficewa daga Gaza
Mashigin Rafah a yau Talata da Falasdinawa ke amfani da shi suna ficewa daga Gaza REUTERS - IBRAHEEM ABU MUSTAFA
Talla

Isra’ila tace sojojin ta sun yiwa birnin Gaza dake dauke da kashi daya bisa 3 na al’ummar Falasdinawa miliyan 2 da dubu 300 kawanya, kuma ana iya afkawa yankin ko yaushe a ci gaba da yunkurin murkushe mayakan Hamas da suka kaiwa garuruwan Isra’ila hari wata guda da ya gabata.

Sanarwar Isra’ilar ta bayyana cewar wa’adin sa’oi 4 ya fara aiki ne daga karfe 10 na safiyar yau agogon Gaza, zuwa karfe 2 na rana, wato daga karfe 12 agogon GMT zuwa karfe 4.

Yadda ake nuna alhini ga 'yan uwan mutanen da Hamas suka kashe a ranar 7 ga watan Oktoba a Birnin Kudus
Yadda ake nuna alhini ga 'yan uwan mutanen da Hamas suka kashe a ranar 7 ga watan Oktoba a Birnin Kudus REUTERS - RONEN ZVULUN

Mazauna yankin sun ce tankunan yakin Isra’ila na ta kusanta yankin cikin dare, yayin da suke amfani da hare haren jiragen sama da kuma amfani da makaman atilare domin share musu hanya.

Sanarwar sojin ta shaidawa Falasdinawa cewar, ‘’domin kare lafiyar ku, ku tashi zuwa yankin Wadi Gaza dake bangaren kudu’’.

Yayin da daukar matakan sojin suka ta’allaka a yankin arewacin Gaza, yankin kudu ma bai tsira daga hare haren ba, ganin yadda hukumomin lafiyar Falasdinu suka bayyana cewar an hallaka mutane 23 a wasu hare hare daban daban guda 2 safiyar yau Talata a Khan Younis da Rafah.

Kwamishinan kare hakkin Bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya, Volcker Turk yace babu abinda ake gani a cikin wata guda da ya gabata da ya wuce zub da jini da ‘dan’dana azaba da lalata kadarori da kuma rashin tabbas.

Jami’in ya bayyana take hakkin Bil Adama a matsayin dalilan da suka haddasa fadadar yakin, yayin da yace su kadai ne kuma za su bude hanyar fita daga cikin irin wannan kunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.