Isa ga babban shafi

Erdogan na Turkiyya ya isa Jamus domin tattaunawa kan yakin Gaza

Shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan ya isa Berlin babban birnin Jamus a Juma’ar nan, inda zai gana da shugabannin kasar kan yakin Zirin Gaza da kuma wasu muhimman batutuwa na kasa da kasa. 

Shugaban Turkiyya Erdogan kenan, lokacin da yake nuna taswirar yankunan Falasdinawa da Isra'ila ta mamaye.
President Erdogan holds a sign showing the evolution of lands of Israel and Palestine on maps at his AK party's group meeting in the Turkish Grand National Assembly in Ankara on October 11, 2023. AFP - ADEM ALTAN
Talla

Shugaba Erdogan ya ziyarci Jamus ne a daidai lokacin da kasashe da hukumomin kasa da kasa, gami da miliyoyin mutane ke cikin fusata, wadanda da dama ke zanga-zangar neman kawo karshen hare-haren Isra’ila a Gaza, inda kawo yanzu ta halaka Falasdinawa sama da dubu 11 da 500. 

An dai tsara Recep Tayyip Erdogan zai fara ganawa da shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier, daga nan ne kuma shugaban na Turkiya zai gana da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz a dai wannan juma’a, inda ake as ran za su tattauna kan neman tsagaita wuta a Zirin Gaza da kuma yadda za a dakile fadadar yakin na Isra’ila da Hamas zuwa wasu kasashen yankin Gabas ta Tsakiya. 

Gabanin ziyarar da ya kai Jamus, shugaban na Turkiya yayi amfani da kakkausan harshe wajen suka kasashen yammacin Turai, ciki har da kasar ta Jamus, kan yadda suke goyon bayan gwamnatin Isra’ila, ba tare da damuwa da laifukan yakin da dakarun kasar ke aikata wa a Zirin Gaza ba. 

Sabbin alkaluma dai sun nuna cewar a halin yanzu Falasdinawa akalla dubu 11 da 500 Isra’ila ta kashe a Gaza, sama da dubu  7 da 800 daga cikinsu mata da yara kanana, tun bayan hare-haren ramuwar da ta kkadamar, bayan harin ranar 7 ga watan Oktoba da mayakan Hamas suka kai mata. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.