Isa ga babban shafi

An kashe 'yan mata kusan dubu 90 da gangan a bara

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mata da ‘yan mata dubu 89 ne aka kashe da gangan a fadin duniya cikin shekarar 2022 kawai. 

Wasu mata a Afghanistan da ke zanga-zangar neman hakkokinsu.
Wasu mata a Afghanistan da ke zanga-zangar neman hakkokinsu. AFP - AHMAD SAHEL ARMAN
Talla

An bayyana haka ne a cikin wani rahoto da Ofishin Hukumar da ke Yaki da Ta’ammali da Muggan Kwayoyi na Majalisar Dinkin Duniya da Manyan Laifuka UNODC hade da Ofishin Hukumar da ke Kare Hakkokin Mata na Majalisar Dinkin Duniya suka fitar game da kashe-kashen mata da ‘yan mata a duniya.

Rahotan ya ce a cikin shekaru 20 da suka gabata, shekarar 2022, ita ce wadda aka fi samun adadi mafi yawa na mata da ‘yan matan da aka kashe ba gaira-ba-dalili.

Rahoton ya kuma ce duk da raguwar da aka samu na yawan kashe-kashen da ya faru a shekarar da ta gabata a fadin duniya, kididdiga na nuna adadin matan da aka kashe a wannan shekarar ya karu. 

Binciken na Majalisar Dinkin Duniya ya kuma bayyana cewa kashi 55 na wadannan mata da ‘yan mata da adadinsu ya kai dubu 48,800, iyalai da makusantansu ne suka kashe su, wato a kowacce rana ana samun akalla mata 133 da wani nasu ya kashe a cikin gidajensu,lamarin da ke kara tabbatar da cewa hatta matan da ke rayuwa a cikin gidan aure, da wadanda ke zama da iyalansu ba su tsira da rayuwarsu ba. 

Rahoton na cewa akwai yiwuwar adadin matan da aka kashe ya zarta hakan saboda karancin bayanai da ake samu a kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.