Isa ga babban shafi

Rasha ta shirya tattaunawa da Amurka da Turai kan Ukraine idan sun so - Putin

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce a shirye yake ya shiga tattaunawar neman zaman lafiya da takawaransa Volodmyr Zelenskyy da Amurka da kuma Turai kan makomar Ukraine idan har suna so, sai dai yayi gargadin cewa Rashan za ta kare muradunta.

Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin © AP - Mikhail Klimentyev摄影
Talla

Putin wanda ya kaddamar da yaki kan Ukraine a farkon shekarar 2022, ya sha nanata cewar kofarsa a bude take ga tattaunawar zaman lafiya.

Sai dai wasu jami'an diflomasiyar kasashen yammacin Turai sun ce shugaban na Rasha yana jiran ganin sakamakon zaben shugaban Amurka a watan Nuwamba ne kafin ya aiwatar da yunkurin shiga tattaunawar neman sulhun da gaske.

A farkon makon nan ne dai Putin ya yi watsi da ikirarin da takwaransa na Amurka Joe Biden yayi kan cewar Rasha za ta kai wa rundunar tsaro ta NATO hari, da zarar ta samu nasara a yakin da take yi a Ukraine.

Biden yayi ikirarin nasa ne a farkon wannan wata, a lokacin da yake rokon ‘yan majalisar dokokin Amurka da su kara yawan tallafi ga Ukraine, wadda yayi gargadin cewar da zarar Rasha murkushe ta, to fa kan kasashen NATO za ta koma, batun da shi kuma a martaninsa, shugaba Putin ya bayyana a matsayin zancen banza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.