Isa ga babban shafi

Hare-haren Rasha a kudancin Ukraine sun hallaka mutane 4

Wasu hare-hare da Rasha ta kai yankin Kherson  da ke kudancin Ukraine cikin sa’oi 24, sun kashe mutane 4 da raunata 9, kamar yadda hukumomin yankin suka tabbatar.

Shugaban Ukraine  Volodymyr Zelensky, yayi Allah wadai da harin Rasha wanda ya kashe mutane 4 a Kharson.
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, yayi Allah wadai da harin Rasha wanda ya kashe mutane 4 a Kharson. AFP - -
Talla

Gwamnan yankin Oleksandr Prokudin ya ce daga jiya asabar zuwa yau lahadi, Rasha ta kai hare-hare 71 wanda suka fada kan gidajen mutane da asibitoci da kuma makarantu.

Prokudin ya ce daga cikin wadanda suka rasa rayukansu, akwai mai shekara 87 da matarsa mai shekara 81, sannan masu aikin ceto suka gano gawar wani a karkashin burabuzai.

Shugaban kasar Volodymyr Zelensky yayi Allah wadan da harin da ya kira dana ta’addanci, wanda ake kaiwa don salwantar da rayuka da lalata kayan gwamnati.

Zelensky ya ce da zarar an dakatar da kai hare-haren, za a gaggauta gyara wutar lantarkin yankin don al’umma su rinka samun dumi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.