Isa ga babban shafi
YAKIN RASHA DA UKRAINE

Rasha ta kaddamar da harin sama sau 158 a birnin Kyiv cikin dare

Rasha ta kaddamar da daya daga cikin manyan hare-haren makami mai linzami kan Ukraine, inda ta kashe fararen hula 18, tare da raunata wasu fiye da 130 bayan ta kai hari kan wasu gine-gine da ke kudu maso yammacin birnin Kyiv, kamar yadda hukumomin Ukraine suka tabbatar.

yadda harin makami mai linzami ta sama ke sauka a birnin Kyiv daga Rasha, ranar 29 ga Disamba, 2023.
yadda harin makami mai linzami ta sama ke sauka a birnin Kyiv daga Rasha, ranar 29 ga Disamba, 2023. REUTERS - GLEB GARANICH
Talla

Ma'aikatar harkokin wajen Ukraine ta ce babban harin da aka kai ta sama a karshen shekara ya nuna cewa bai kamata a yi maganar sulhu da fadar Kremlin ba, a daidai lokacin da rashin tabbas ya tabbata kan goyon bayan kasashen yamma ga gwamnatin Kyiv.

A Kyiv babban birnin kasar akalla mutane uku ne aka ruwaito sun mutu sannan ashirin da biyu aka tabbatar sun jikkata bayan harin da aka kai kan wasu gine-ginen gidaje inda suka rubta a kansu.

Ministan harkokin wajen kasar Dmytro Kuleba ya ce, miliyoyin al’ummar Ukraine sun farka da karar fashewar abubuwa, inda ya bukaci kasashen kawance da su ci gaba da bayar da taimakon soja.

Wata mata da ke zaune a birnin Kyiv, mai suna Mariia ta shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa amon fashewar wani abu, ya tashe daga bacci, inda ta yi gaggawa neman mafaka a bandakinta.

Rundunar sojin saman kasar, ta ce ta harbo makamai masu linzami 87 da jirage marasa matuka 27 daga cikin jiragen sama 158 da Rasha ta harba wa kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.