Isa ga babban shafi

Japan zata kwashe mutane daga yankin Noto saboda barazanar Tsunami

A Litinin din nan ce wata girgizar kasa mai karfin maki 7.5 ta faru a tsakaniyar kasar Japan, wacce ta haifar da barazanar samuwar Tsunami lamarin da ya sa hukumomi butar jama’a su fice daga yankin.

Yadda wasu hanyoyi suka daddare a yankin da aka samu girgizar kasa a Japan.
Yadda wasu hanyoyi suka daddare a yankin da aka samu girgizar kasa a Japan. AP
Talla

Gidan rediyon kasar NHK ya ce girgizar kasar ta afku a yankin Noto da ke lardin Ishikawa da misalin karfe 4:10 agogon kasar.

Cibiyar kula da girgizar kasa da ke Hawaii, ta ce akwai igiyar ruwan Tsunami da ta taso daga gabar tekun Japan bayan faruwar girgizar kasar.

An kuma tabbatar da cewa guguwar Tsunami mai tsawon mita 1.2 ta isa birnin Wajima da ke lardin Ishikawa.

Sai dai Hukumar Kula da Yanayi ta Japan ta ce ana sa ran Tsunami mai karfin mita biyar za ta isa birnin Noto.

Kimanin gidajen dubu 33 da dari 5 ne suka rasa wutar lantarki bayan faruwar lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.