Isa ga babban shafi

Kotu ta daure tsohon Firaminista Khan da amaryarsa saboda aure cikin idda

Duniya – Wata kotu a kasar Pakistan a yau ta daure tsohon Firaminista Imran Khan shekaru 7 a gidan yari tare da amaryar sa Busra Bibi saboda abinda ta kira sabawa dokokin Islama wajen gudanar da auren su.

A wannan mako kotuna a Pakistan sun daure Imran Khan na shekaru 31 a hukunce hukunce daban daban
A wannan mako kotuna a Pakistan sun daure Imran Khan na shekaru 31 a hukunce hukunce daban daban AP - K.M. Chaudary
Talla

Kotun tace amaryar Khan wadda bazawara ce bata cika iddar watanni 3 ba, kamar yadda addinin Islama ya tanada domin sake aure ga wadda mijin ta ya mutu ko kuma ta bar mijin ta na farko.

Tuni jam’iyyar sa ta PTI ta bayyana hukuncin wanda shine irin sa na 3 da aka daure Khan a cikin wannan mako a matsayin na siyasa domin hana shi shiga zabe.

Sai dai lauyan sa Gohar Ali Khan yace zasu daukaka kara domin kalubalantar hukuncin.

Imran Khan da amaryar sa Bushra Wattoo lokacin da aka daure auren su a birnin Lahore
Imran Khan da amaryar sa Bushra Wattoo lokacin da aka daure auren su a birnin Lahore Pakistan Tehreek-i-Insaaf/AFP

A farkon wannan mako, kotu ta yanke hukuncin daurin shekaru 10 a kan tsohon Firaministan saboda samun sa da laifin bayyana asirin gwamnati, yayin da aka sake yanke masa wani hukuncin na daurin shekaru 14 shi da matar sa Bushra Bibi saboda samun su da laifin cin hanci da kuma sayar da kyaututtukan da aka basu lokacin da yake rike da mukamin Firaminista.

Yanzu haka Khan na tsare a gidan yarin Rawalpindi inda ya kwashe watanni a tsare, yayin da matarsa Bibi da ta gabatar da kan ta ga jami’an tsaro ke tsare a gidan ta dake wajen birnin Islamabad.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.