Isa ga babban shafi

Harin kunar bakin wake ya hallaka mutane 26 a Pakistan

Wani harin kunar bakin wake ya allaka mutane 26 cikin su 6 jami’an tsaro ne, tare da jikkata wasu 25 a Pakistan da safiyar yau Talata.

Kungiyar ta balle ne daga cikin TTP wadda aka rusa a baya-bayan nan
Kungiyar ta balle ne daga cikin TTP wadda aka rusa a baya-bayan nan © Shaheed Nawab Ghous Bakhsh Raisa / Reuters
Talla

Bayanai sun nuna cewa maharin ya farwa wani taron jama’a cikin wani gini, kuma bayan ya tarwatsa bam din da ke daure a jikin sa ne sauran abokan aikin sa suka bude wuta.

Da yake karin haske shugaban rundunar ‘yan sandan yankin Kamal Khan ya ce bayan da maharan suka bude wuta, jami’an tsaro sun mayar musu da martani, dalilin da ya sa yan sanda 6 suka mutu nan take, yayin da wasu da dama suka jikkata.

Harin dai ya auku ne a yankin Dera Isma’il Khan a lardin Khyber Pakhtunhkwa yankin da a baya ke karkashin dandazon mayakan Taliban.

Wannan yanki na fama da hare-haren ‘yan ta’adda na sabuwar kungiyar Tehreek-e-Jihad wadda ta balle daga kungiyar TTP, kuma tuni kungiyar ta dauki alhakin kai harin.

Har yanzu dai babu wani cikakken bayani daga gwamnati ko kuma jami’an kasar a hukumance, sai dai bayanan farko na nuna cewa adadin wadanda suka mutu ka iya karuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.