Isa ga babban shafi

Harin kunar bakin wake kan masu Mauludi a Pakistan ya kashe mutane 52

Rahotanni daga Pakistan na cewa akalla mutane 52 sun mutu a harin kunar bakin waken da aka kai kan dandazon masu taron Mauludi don tunawa da zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabin rahma tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi, yau Juma’a a lardin Bolichistan.

Gomman mutane ne yanzu haka ke cikin mawuyacin hali kari kan mutum 52 da suka mutu a harin na yau Juma'a.
Gomman mutane ne yanzu haka ke cikin mawuyacin hali kari kan mutum 52 da suka mutu a harin na yau Juma'a. © Shaheed Nawab Ghous Bakhsh Raisa / Reuters
Talla

Majiyoyin labarai daga yankin na Bolichistan sun tabbatar da karuwar alkaluman a harin na yau juma’a da aka kai gab da babban masallachin yankin Mastung wanda da farko ya kashe mutane 42 tare da jikkata mutane akalla 80 ciki har da wadanda ke cikin mawuyacin hali.

Karamin ministan Lardin na Balochistan Zubair Jamali ya tabbatar da cewa harin ya rutsa da tarin mutane ciki har da kananan yara da ke shagalin bikin tunawa da ranar zagayowar haihuwar fiyayyen halitta Annabin rahma tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi.

Rahotanni sun bayyana cewa dan kunar bakin waken ya yi damarar bom tare da shiga cikin dandazon mutanen da ke halartar taron Mauludin inda ya tayar da bom din gab da motar babban sufuritandan ‘yan sandan yankin da ke bayar da tsaro a wajen Nawaz Gishkori.

Har zuwa yanzu dai babu kungiyar da ta dauki alhakin harin na yau Juma’a, sai dai kungiyar IS ta yi kaurin suna wajen kai makamantan hare-haren yayinda cikin gaggawa kungiyar TTP ta nesanta kanta da harin.

Ko a watan Yulin da ya gabata, sai da wani harin ta’addanci ya hallaka sojojin Pakistan 12 a Lardin na Bolichistan kari kan kisan jami’an tsaro 9 cikin watan Maris duk dai a yankin mai fama da matsalar tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.