Isa ga babban shafi

Yau ake cika watanni 4 cur da fara luguden wutar Isra’ila a Gaza

Rafah ya kasance marika ta karshe da ke hannun Hamas a Gaza bayan da Isra’ila ta rushe fiye da kashi 2 bisa 3 na gine-ginen zirin na Gaza dalilin da ya tilastawa iyalai miliyan daya da dubu 400 komawa rayuwa a sansanonin wucin gadi.

Isra'ila ta rushe fiye da kashi 2 bisa 3 na gine-ginen yankin Gaza da suka kunshi asibitoci da makarantu da wuraren ibada.
Isra'ila ta rushe fiye da kashi 2 bisa 3 na gine-ginen yankin Gaza da suka kunshi asibitoci da makarantu da wuraren ibada. © Ibraheem Abu Mustafa / Reuters
Talla

Dai dai lokacin da ake cika watanni 4 cur da faro luguden wutar Isra’ilan a Gaza alkaluman da ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta fitar ta ce Isra’ilan ta kashe mutanen da yawansu ya tasamma dubu 30 baya ga jikkata wasu kusan dubu 70 a bangare guda ake ci gaba da neman wasu fiye da dubu 8 da har zuwa yanzu ba a kai ga gano gawarwakinsu ba.

Ko a safiyar yau Laraba, Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare Gaza tare da jefa bama-bama kan yankunan fararen hula inda sojojinta ke ci da gaba da kutsawa Rafah dai dai lokacin da karancin abinci da ruwan sha baya ga magunguna ke ci gaba da tsananta a yankin.

Yanzu haka dai bangarorin Isra’ila da Hamas sun amince da komawa teburin tattaunawa don tsagaita wutar dindindin a yakin ko da ya ke Qatar ta bayyana cewa zai dauki lokaci gabanin iya cimma jituwa.

Matakin amincewa da tsagaita wutar na zuwa ne a ziyarar da Antony Blinken na Amurka ke yi a yankin na gabas ta tsakiya da ke matsayin karo na 4 tun bayan faro yakin a ranar 7 ga watan Oktoban da ya gabata.

Duk da yadda Kotun duniya ta bukaci Isra’ila ta mutunta dokokin kare hakkin dan adam, har zuwa yanzu daruruwan rayukan fararen hula na ci gaba da salwanta kowacce rana.

Wasu bayanai a safiyar yau sun bayyana yadda Isra'ilan ke kafa tantuna don datse hanyoyin da za su bayar da damar shigar da kayan agaji Gaza, yankin da yunwa ke galabaitar da al'ummarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.