Isa ga babban shafi

Faransa na jagorantar tattaunawar bukatar tsagaita wuta a Gaza

Faransa na karba bakoncin taron tattaunawa don samar da mafita wajen tsagaita wuta a yakin da Isra’ila ke yi a Gaza da zuwa yanzu ya kashe mutane dubu 29 da 410 baya ga jikkata wasu dubu 69 da 465.

Har zuwa safiyar yau Juma'a Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare Gaza da wasu sassa na Rafah.
Har zuwa safiyar yau Juma'a Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare Gaza da wasu sassa na Rafah. AFP - SAID KHATIB
Talla

Tattaunawar dai na samun wakilcin kasashen Amurka da Qatar da kuma Masar sai ita Isra’ilan da ke kai hare-haren, ba tare da wakilci daga Falasdinu ba.

Haka zalika taron na zuwa bayan makamantansa a kasashe daban-daban wadanda ba su kai ga nasarar tsagaita wutar ba.

Tun farko Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi watsi da kudirin Hamas na ganin an tsagaita wutar na tsawon watanni 4 da rabi wanda zai bayar da damar ficewar dakarun kasar ta Yahudu daga Gaza, maimakon haka ya sanya ranar faro azumin watan Ramadana a matsayin lokacin da zai faro sabon farmaki a Rafah.

Za a shafe tsawon kwanakin karshen mako ana gudanar da tattaunawar a Paris wadda ake saran ta kai ga nasarar tsagaita wuta bayan rushewar makamanciyar tattaunawar makwanni 2 da suka gabata.

Taron na zuwa a dai dai lokacin da tsohuwar minister harkokin wajen Faransar Catherine Colonna ke jagorancin wata kungiya mai zaman kanta da za ta gudanar da bincike kan sahihanci hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta yankin Falasdinu a kasancewarta ‘yar baruwanmu kamar yadda doka ta kafa ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.