Isa ga babban shafi

Matsanancin karancin abinci zai ta'azzara mutuwar kananan yara a Gaza - MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta ce matsanancin karancin abinci da rashin abinci mai gina jiki da ta’azzarar cutuka na iya ingiza karuwar mutuwar kananan yara a Zirin Gaza.

Babban Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres.
Babban Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres. REUTERS - NAVESH CHITRAKAR
Talla

Makwanni 20 da fara wannan yaki tsakanin Isra’ila da Hamas a yankin Zirin Gaza, hukumomin Majalisar Dinkin Duniya sun yi kashedin cewa akwai matsanancin karancin abinci da tsaftataccen ruwa a yankin na Falasdinawa, inda suka kara da cewa akasarin kananan yara sun kamu da cutuka masu yaduwa.

Mataimakin shugaban ayyukan jinkai a Assusun kula da kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya, Ted Chaiban ya ce Zirin Gaza zai fuskanci mutuwar kananan yara, wadda zai ta’azzara halin da ake ciki a halin yanzu.

Wani Nazari na hadin gwiwa da hukmomin Majalisar Dinkin Duniya suka yi na nuni da cewa, kashi 90 na kananan yara daga shekaru 5 zuwa kasa a Gaza sun kamu da cutuka masu yaduwa.

Kashi 70 na kananan yaran sun yi fama da cutar amai da gudawa gabanin wannan nazari, abin da ke nuni da kari har ninki 23 idan aka kwatanta da shekarar 2022.

Harin da mayakan Hamas suka kai Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda  ya yi sanadin mutuwar mutane dubu 1 da 160 ne ya haddasa yakin Gaza

Mahukuntan Zirin Gaza sun ce hare-haren da Isra’ila ke kai wa yankin ya yi sanadin mutuwar  mutane dubu 29 a halin da ake ciki.

Tun da aka fara wannan yakin, Zirin Gaza ya fada cikin matsalar karancin abinci mai gina jiki, sakamakon yadda aka takaita shigar da kayayyakin agaji yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.