Isra'ila ta sake aukawa kudancin Gaza da luguden wuta
Luguden wutar da Isra’ila ke yi a birnin Rafah na kudancin Zirin Gaza ya shafi gidaje, al’amarin da ke ta’azzara abin da kungiyoyin agaji suka bayyana a matsayin mummunan yanayi, duk kuwa da kokarin da ake na cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.
Wallafawa ranar:
Barin wutar da Isra’ilar ke yi ya lalata wani gida, kana ya huda wani katafaren rami a gabashin birnin Rafah, inda akalla al’ummar Gaza su kimanin miliyan 1 da dubu dari 4 ke neman mafaka daga rikicin da ake yi.
Wannan yaki ya barke ne bayan da mayakan Hamas suka kai wani hari cikin Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata, lamarin da ya yi sanadin sama da mutane dubu daya.
A asibitin Najjar da ke kudancin birnin Rafah , masu zaman makoki sun rungume gawarwakin wasu kananan yara da aka rufe fuskokinsu da farin kyalle.
Bayanai sun ce, an yi luguden wuta a gundumar Zeitun da ke makwabtaka da Rafah, inda aka jibge tankokin yaki, da sojoji.
Sojojin sun ce jirage masu saukar ungulu na ci gaba da taimakawa ‘dakarun da aka tura yankin, domin yakar Hamas.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu