Isa ga babban shafi

Harin 'yan ta'adda ya hallaka sojojin Pakistan 7

Sojojin Pakistan 7 da wasu 'yan kungiyar da ke dauke da makamai 6 ne suka rasa rayukansu a Asabar din nan, a wani hari da aka kai wa wani sansanin jami’an tsaro da ke kusa da kan iyakar kasar da Afganistan.

Sojojin Pakistan 7 suka rasa rayukansu, a wani hari da aka kai wa wani sansanin jami’an tsaro da ke kusa da kan iyakar kasar da Afganistan.
Sojojin Pakistan 7 suka rasa rayukansu, a wani hari da aka kai wa wani sansanin jami’an tsaro da ke kusa da kan iyakar kasar da Afganistan. © Asim Tanveer / AP
Talla

A cewar wata sanarwa da rundunar sojin kasar ta fitar, ta ce mambobin wata kungiya masu dauke da makamai ne suka kai wa jami’ansu hari a kusa da Mir Ali da sanyin safiyar Asabar din nan.

'Yan ta'addar sun kai hari da wata mota makare da bama-bamai a ofishinmu, sannan daga bisani wasu hare-haren kunar bakin wake suka biyo baya, wanda ya kai ga rushewar wani bangare na ginin.

Sanarwar ta ce, a yayin musayar wutar da aka yi tsakanin sojoji da maharan, wani soja mai mukamin Laftanar dan shekaru 39 da kuma wani mai mukanin Kyaftin dan shekaru 23 sun rasa ransu.

A banagren maharan kuwa, mutanensu 6 ne suka mutu.

A baya Pakistan ta yi fama da hare-haren bama-bamai kusan kullum, lamarin da ya sanyata gudanar da wani gagarumin aikin sintirin soji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.