Kasashe sun yi wa Isra'ila caa bayan harin da ta kaiwa jami'an bada agaji
Kungiyar Tarayyar Turai da wasu kasashe da kungiyoyin bada agaji, na ci gaba da Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai wa tawagar wata kungiyar bada agajin abinci ta Amurka ta World Central Kitchen, da ya yi sanadiyar mutuwar jami’anta 7 a Gaza.
Wallafawa ranar:
Jami’in kula harkokin kasashen waje na kungiyar Tarayar Turai Josep Borrell, ya ce duk da bukatar bai wa fararen hula da jami’an bada agaji kariyar da aka yi, har yanzu ana ci gaba da asarar rayukansu.
Daga cikin wadanda suka rasa rayukansu a harin na jiya Litinin, akwai ‘yan kasashen Australia da Birtaniya da Poland da wani da ke dauke da takardar zama dan kasashen Amurka da Canada sai kuma Bafalasdine.
A cikin wata sanarwa da kakakin Majalisar Tsaron Amurka Adrienne Watson ta fitar, ta ce fadar White House ta kadu da harin da aka kaiwa jami’an bada agaji, don haka ta ce dole ne a bai wa masu irin wannan aiki kariya da kuma bada damar isar da kayan abinci.
Firaministan Australia Anthony Albanese, ya yi Allah wadan da wannan hari, inda ita kuma Poland ta rubutawa Isra’ila wasakar da ke cewar hare-harenta sun saba wa dokokin bada agaji na duniya.
Kasashen Birtaniya da Spain da Masar da Belgaum da Cyprus da Iran da Jordan da Scotland da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO da sauransu, sun bukaci a gudanar da bincike kan lamarin da suka bayyana a matsayin wanda ya sabawa dokokin kasa da kasa.
Tuni dai kakakin ma’aikatar tsaron Isra’ila Daniel Hagari ya fidda wani sakon bidiyo, inda yake jajantawa kasashen da suka rasa ‘yan kasarsu a wannan hari.
Duk da cewa bai fito fili ya bayyana cewar su ne suka dauki alhakin kai harin ba, ya tabbatar da cewar za su gudanar da bincike don kaucewa sake faruwar hakan a nan gaba.
Kungiyar bada agaji ta Red Crescent ta Falasdinu, ta ce za a dauki gawarwanin mutanen zuwa asibitin Abu Youssef al-Najjar da ke Rafah na Masar.
Jami’an kungiyar ta WCK sun hadu da ajalinsu ne a lokacin da suke kan hanyar kai kayan agaj yankin Tsakiyar Gaza, inda Isra'ila ta kai wa motocinsu hari duk kuwa da hoton tambarin Kungiyar WCK da ke like a jikinsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu