Isa ga babban shafi
YAKIN-GAZA

Amurka ta gargadi Isra'ila a kan ci gaba da kashe fararen hula a Gaza

Duniya – Kasar Amurka ta bukaci Isra’ila da ta gaggauta tsagaita wuta a hare haren da take kaiwa Gaza da kuma bude kofofin kai kayan agaji, ko kuma ta sake matsayin manufofin ta a kan kasar.

Joe Biden și Benjamin Netanyahu
Shugaba Joe Bide da Firaminista Benjamin Netanyahu AP
Talla

Shugaban kasar Joe Biden ya shaidawa Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a tattaunawar da suka yi ta waya yau alhamis, sakamakon kazamin harin da Isra’ilar ta kai a kan motocin ma’aikatan agaji na kasashen duniya wanda ya yi sanadiyar hallaka 7 daga cikin su.

Tuni wannan harin ya gamu da suka daga kasashen duniya, musamman kasashen Birtaniya da Canada da kuma Australia, kasashen da ma’aikatan agajin suka fito.

Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron Amurka, John Kirby yace Biden ya jaddadawa Netanyahu cewar matsayin Amurka na taimakawa Israilar kare kan ta na nan daram, amma kuma manufar kasar na iya sauyawa ganin yadda ake ci gaba da kashe fararen hula ba tare da kaukauatawa ba.

Biden ya bukaci Isra’ilar da ta gaggauta gabatar da ingantaccen Shirin tsagaita wuta da kuma kaucewa kai hari a kan fararen hula tare da bude kofofin kai kayan agaji ga mabukata tare da bai wa masu aikin agaji damar gudanar da ayyukan su.

Shugaban Biden na ci gaba da fuskantar matsin lamba a ciki da wajen kasar Amurka, inda a ranar Talata shugabannin Musulmin kasar suka ki amsa gayyatar zuwa bude bakin azumin watan Ramadan a fadar as.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.