Isa ga babban shafi
Yemen-Daular Larabawa

An kashe mutane uku a harin Daular Larabawa

Mutane uku sun rasa rayukansu a wani hari da ake zargin mayakan Huthi na Yemen da kaddamarwa a birnin Abu Dhabi da ke Hadaddiyar Daular Larabawa a yau Litinin.

Ana zargin mayakan Huthi da kaddamar da farmakin.
Ana zargin mayakan Huthi da kaddamar da farmakin. - AFP
Talla

Rahotanni na cewa, mayakan sun yi amfani da jirgi mara matuki wajen kaddamar da farmakin, lamarin da ya yi sanadiyar ajalin wasu mutane biyu ‘yan asalin India da kuma mutun guda dan asalin Pakistan, bayan harin ya haddasa gobarar tankar man fetur.

Kazalika an samu tashin gobara a wani yanki da ake gyaran sa a filin jiragen sama na birnin Abu Dhabi.

Jami’an ‘yan sanda sun ce, an gano kananan jiragen sama marasa matuka guda biyu a wuraren da gobarar ta tashi, inda suke ganin babu makawa, hare-hare ne da aka kaddamar da su da gan-gan a Hadaddiyar Daular Larabawa wadda ta fi zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

Kawo yanzu ‘yan tawayen Huthi na Yemen masu samun goyon bayan Iran ba su fito karara  sun dauki alhakin wannan farmakin ba, amma mai magana da yawun dakarun na Huthi ya sanar  da wani aikin soji da suke  shirin gudanarwa a Hadaddiuar Daular Larabawa wadda ke cikin rundunar hadin guiwa  mai goyon bayan gwamnatin Yemen.

A can baya mayakan na Huthi sun yi barazanar kai hari kan biranen Abu Dhabi da Dubai.

Hare-haren jiragen sama marasa matuka, wabi abu ne da ke alamta irin farmakin da mayakan Hiuthi suka saba kaddamarwa kan Saudiya wadda aminya ce ga Hadaddiyar Daular Larabawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.