Isa ga babban shafi

'Yan majalisar Iraqi sun sake gazawa wajen zaben sabon shugaban kasa

‘Yan majalisar dokokin Iraqi sun sake gazawa wajen zaben sabon shugaban kasa a yau Asabar, sakamakon rashin samun isassun kuri’un yin hakan a zaben da suka yi a zauren majalisar dokokin kasar, lamarin da ya kara dagula yanayin rashin tabbas na siyasar da suke ciki.

Zauren majalisar dokokin kasar Iraqi da ke birnin Bagadaza.
Zauren majalisar dokokin kasar Iraqi da ke birnin Bagadaza. © AP/Iraqi Parliament Media Office
Talla

Tun da farko dai majalisar ta fitar da jerin sunayen 'yan takara 40 na karshe da ke neman darewa bisa shugabancin kasar ta Iraqi, inda takara tafi zafi tsakanin shugaba mai ci Barham Saleh, na jam’iyyar PUK, da Rebar Ahmed na jam'iyyar adawa ta KDP.

Sai dai rashin yawan kuri'un da aka kada da ake bukata da adadinsu ya kai kashi biyu bisa uku na 'yan majalisar 329 ya sanya sake samun jinkiri kan zaben sabon shugaban, kokarin da ake faman yi tun  cikin watan Fabarairu.

Bayanai sun ce ‘yan majalisar 202 ne kawai suka halarci zaben sabon shugaban kasar na Iraqi, abinda ya sanya dole a shirya wani sabon zama a ranar Laraba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.