Isa ga babban shafi

Blinken na ziyara a kasashen Larabawa

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya kai ziyara Morocco domin tattauna batun tsaron yankin, yayin da kuma zai gana da Yarima na Hadaddiyar Daular Larabawa Mohammed bin Zayed al-Nahyan.

Anthony Blinken
Anthony Blinken AFP - BRENDAN SMIALOWSKI
Talla

A dai daren Litinin ne Blinken ya baro Isira’ila bayan da ya yi wata ganawa da jami’an diflomasiya na kasashen Hadaddiyar Daular larabawa da  Moroco da Bahrain da kuma Masar game da alakarsu da Isira’ila.

Kafin ganawarsa da Firaministan Moroco Aziz Akhannouch, Blinken ya yi wata ganawa da Ministan Harkokin Wajen kasar Nasser Bourita akan abin da ya shafi tsaro ciki harda yaki da kungiyar IS da kuma Al-Qaida.

A daren yau ne ake kuma saran Blinken zai gana da Yarima Mohammed bin Zayed al-Nahyan a gidansa da ke Moroco wacce ke zuwa a kokarin da Amurka ke yi na farfado da dadaddiyar alakar dake tsakanin su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.