Isa ga babban shafi

Muna kan hanyar samar da kasashe 2 tsakanin Isra'ila da Falasdinu - Biden

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce aniyar kasar ta lalubo masalahar samar da kasashe 2 a tsakanin Isra’ila da Falasdinu na nan daram.Shugaban Amurka yana jawabi ne a yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas a yankin gabar Yamma da Kogin Jordan a Juma’ar nan.

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas da Shugaban Amurka Joe Biden suna gaisawa a garin Bethlehem da ke gabar yammacin kogin Jordan, Juma'a, 15 ga Yuli, 2022. (AP Photo/Evan Vucci)
Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas da Shugaban Amurka Joe Biden suna gaisawa a garin Bethlehem da ke gabar yammacin kogin Jordan, Juma'a, 15 ga Yuli, 2022. (AP Photo/Evan Vucci) AP - Evan Vucci
Talla

Shugaba Biden ya shaida wa Mahmoud Abbas na Falasdinu a birnin Bethlehem cewa, Amurka ba za  ta yi kasa a gwiwa ba a kan kudirinta na lalubo masalaha a game da rikicin da aka shafe shekaru da dama ana yi tsakanin Isra’ila da Falasdinawa.

Ko da yake ya bayyana goyon baya ga masalaha ta samar da kasashe biyu a tsakanin al’ummomin da ke rikici da juna, shugaba Biden ya ce har yanzu akwai sauran rina a kaba a kan wannan burin.

Sai dai  akwai yiwuwar wadannan kalamai na Biden ya sanyaya gwiwar Falasdinawa, wadanda ke jiran ganin Amurka ta matsa wa Isra’ila lamba wajen sake farfado da tattaunawar, wadda ta ruguje fiye da shekaru 10 da suka wuce.

Shi ko shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas, ya ce batun lalubo zaman lafiya zai fara ne da kawo karshen mamayar da isra’ila ke yi a yankunan Falasdinawa, yana mai cewa a shirye yake ya ba wa shugabannin Israila goyon baya don cimma zaman lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.