Isa ga babban shafi

Sojoji sun sanya dokar hana fita a kasar Iraqi

Sojoji a kasar Iraqi sun kafa dokar hana fita a fadin kasar daga yau litinin sakamakon rikicin da ya barke sakamakon kutsa kai da magoya bayan fitaccen malamin kasar Moqtada al Sadr suka yi, zuwa yankunan dake dauke da gine gine gwamnati da kuma ofisoshin diflomasiya.

Magoya bayan fitaccen malamin Shi'a Muqtada al-Sadr, kenan lokacin da suke gudanar da zanga-zanga a Iraq.
Magoya bayan fitaccen malamin Shi'a Muqtada al-Sadr, kenan lokacin da suke gudanar da zanga-zanga a Iraq. AP - Nabil al-Jurani
Talla

Rahotanni sun ce an ji karar harbe harbe lokacin da magoya bayan malamin suka je kusa da fadar shugaban kasa, yayin da Sadr ya sanar da kawo karshen harkokin siyasar.

Wannan sanarwar ta sanya magoya bayan malamin shiga zanga zangar da ta kai su ofisoshin gwamnati, inda suke daga tutar kasar suna daukar hoto, abinda ya sa jami’an tsaro suka harba hayaki mai sa hawaye.

An ga masu zanga zangar na furta sunan malamin, Moqtada, Moqtada, wanda a baya ya bukaci rusa majalisar dokokin kasar domin gudanar da sabon zabe.

Tun bayan zaben yan majalisun da akayi a watan Oktobar bara, aka samu barakar da ta hana kafa gwamnati ko Firaminista ko kuma shugaban kasa, saboda rashin jituwar dake tsakanin bangarorin siyasar kasar.

Rahotanni sun ce biyu daga cikin magoya bayan al Sadr sun mutu, yayin da wasu 22 suka samu raunuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.