Isa ga babban shafi

Mohammed al-Sudani ya zaman sabon Firaministan Iraqi

Sabon zababben shugaban kasar Iraki ya nada dan Mohammed Shi'a al-Sudani a matsayin wanda sabon firaminista, inda ya dora masa alhakin sasanta bangarorin 'yan Shi'a da ke gaba da juna tare da kafa gwamnati bayan shafe shekara guda ana gwabza fada a kasar.

Sabon Firaministan Iraqi Muhammad Shia al-Sudani
Sabon Firaministan Iraqi Muhammad Shia al-Sudani ©AFP
Talla

Dan shekaru 52, wanda ke samun goyon bayan masu fafutuka da ke samun goyon bayan Iran, ya sha alwashin kafa gwamnati cikin gaggawa amma zai fuskanci babban aiki na samun galaba a kan abokan hamayyarsu, wato miliyoyin mutane masu ra'ayin rikau da ke goyon bayan fitaccen malamin nan Moqtada Sadr.

Lokacin da aka fara gabatar da shawarar nada Sudani a watan Yuli, matakin ya haifar da zanga-zangar da mabiya Sadr suka yi, wadanda suka keta yankin Green Zone tare da mamaye majalisar dokokin kasar.

Akalla mutane 10 ne suka samu raunuka, ciki har da jami’an tsaro shida da ke bayar da kariya ga ‘yan majalisa, da kuma wasu fararen hula hudu a wata gunduma da ke kusa da babban birnin kasar.

Cibiyoyin dimokuradiyya da aka gina a Iraki mai arzikin man fetur tun bayan harin da Amurka ta kai a shekara ta 2003 wanda ya hambarar da mulkin Saddam Hussein na ci gaba da kasancewa cikin rauni, inda ake ganin makwabciyarta Iran tana da tasiri mai girma da kasancewar hakan.

Sama da shekara guda ke nan, Iraki ke karkashin gwamnatin rikon kwarya da ke tunkarar matsalolin da suka hada da rashin aikin yi, lalata ababen more rayuwa, cin hanci da rashawa da kuma tasirin sauyin yanayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.