Isa ga babban shafi

An kashe jami'an Iraqi tara a harin da ake zargin na IS ne

Wasu ‘yan bindiga a arewacin kasar Iraki sun tarwatsa wata motar da ke dauke da ‘yan sanda tare da bude wuta inda suka kashe mutane tara, kamar yadda majiyar ‘yan sanda ta bayyana a ranar Lahadi.

IS ta rasa sansaninta na karshe da ta kafa a Syria, kusa da iyakar Iraki, a cikin 2019.
IS ta rasa sansaninta na karshe da ta kafa a Syria, kusa da iyakar Iraki, a cikin 2019. 路透社照片
Talla

Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, wanda ya kasance daya daga cikin mafi muni da aka taba yi a kasar ta Iraki cikin 'yan watannin nan.

Haka zalika an kai harin kai tsaye da kananan makamai a kusa da kauyen Shalal al-Matar, kamar yadda wani jami’in ‘yan sandan ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP, yana mai alakanta harin da kungiyar IS.

“An kashe wani maharin kuma muna neman sauran mambobin kungiyar masu dauk da makaman,” in ji jami’in.

Hukumomin tsaro sun ruwaito cewa ‘yan sanda biyu ne suka samu raunuka daga baya suka mutu, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa tara.

Mayakan IS masu da’awar jihadi sun kwace yankuna da dama na Iraqi da Syria a shekarar 2014, inda suka ayyana “Khalifanci” kafin a murkushe su a karshen shekarar 2017 wanda sojojin Iraqi tare da goyon bayan kawancen sojan da Amurka ke jagoranta suka samu nasarar murkushe su.

IS ta rasa sansaninta na karshe da ta kafa a Syria, kusa da iyakar Iraki, a cikin 2019.

Firaministan Iraki Mohammed Shi'a al-Sudani ya yi Allah-wadai da tashin hankalin a matsayin harin ta'addanci.

Yakamata jami'an tsaro su nuna taka tsan-tsan, su binciki tituna a tsanake, kada su ba da dama ga 'yan ta'adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.