Isa ga babban shafi

Wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da wani mai fafutukar kare muhalli a Iraqi

Wasu mutane dauke da makamai sun yi garkuwa da wani fitaccen dan gwagwarmayar Iraqi da ke fafutukar kare  muhalli na Iraqi a kudancin Bagadaza babban birnin kasar, kamar yadda iyalansa suka sanar.

Wasu daga cikin masu zanga-zanga a kasar Iraki
Wasu daga cikin masu zanga-zanga a kasar Iraki AP - Hadi Mizban
Talla

Jassim al-Assadi, mai shekaru 65, shugaban kungiyar kare muhalli ta Nature Iraq, ya bayyana akai-akai a kafafen yada labarai na cikin gida da na waje, domin wayar da kan jama'a game da barazanar da yankin kudancin kasar ke fuskanta, yankin da ya yi fama da fari na tsawon shekaru.

Assadi "yana tuki a kan babbar hanyar Hilla zuwa Bagadaza" a safiyar Laraba lokacin da aka sace shi, kamar yadda dan uwansa Nazim ya shaida wa AFP.

Nazim Assadi ya kara da cewa "Dan uwana yana tare da shi." Sun bar shi a hanya.

Iyalin dai ba su ji ta bakin Assadi ba tun daga lokacin kuma ‘yan sanda na kan bincike, dan’uwan ya ce masu garkuwa da mutanen ba su tuntubi wani dangi ba.

Wani jami’in tsaron Iraqi da ya bukaci a sakaya sunansa saboda ba a ba su izinin yin magana da manema labarai ba, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa iyalan sun ba da rahoton bacewar Assadi.

Yayin da Iraqi ta samu kwanciyar hankali bayan shekaru da dama na rikici da tashe-tashen hankula, kisan gilla da sace masu fafutuka da jami'ai ya zama ruwan dare gama gari.

Kungiyoyin fararen hula na Iraki sun yi Allah wadai da ci gaba da kasancewar bangarorin da ke dauke da makamai a fadin kasar da kuma yawaitar makamai, yayin da rikice-rikicen kabilanci ke haifar da tashe-tashen hankula.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.