Isa ga babban shafi

Kasashen Duniya sun kalubalanci jawabin Ministan kudin Isra'ila

Ministan kudi na Isra'ila a jiya asabar ya yi amay ya lashe biyo bayan kalamansa inda ya yi kira da a "share" wani garin Falasdinu bayan an kashe wasu 'yan Isra'ila biyu mazauna wurin. 

Wasu daga cikin masu zanga-zanga a yankin gabas ta tsakiya
Wasu daga cikin masu zanga-zanga a yankin gabas ta tsakiya AP - Ohad Zwigenberg
Talla

A ranar 26 ga watan Fabarairu ne aka bindige matasan ‘yan gudun hijirar biyu a cikin motarsu a garin Huwara da ke arewacin gabar yammacin kogin Jordan, lamarin da ya haifar da hare-haren da ‘yan Isra’ila suka kai kan garin Falasdinu. 

Bezalel Smotrich, shugaban jam'iyyar Sahayoniya mai tsattsauran ra'ayi kuma memba na kawancen firaminista Benjamin Netanyahu ya fada a ranar Laraba cewa: "Ina ganin ya kamata a kawar da kauyen Huwara." 

Yankin Ramallah
Yankin Ramallah REUTERS - MOHAMAD TOROKMAN

Kalaman na Smotrich sun janyo Allah wadai da kasashen duniya, inda babban jami'in kare hakkin bil'adama na Majalisar Dimkin Duniya Volker Turk ya yi tir da su a matsayin "lalaci marar fahimta na tunzura jama'a da tashin hankali." 

Washington, wacce ke da alaka da Isra'ila, ta yi karin haske game da martanin da ta mayar kan kalaman Smotrich. 

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka Ned Price ya shaida wa manema labarai cewa: "Sun kasance marasa alhaki, sun kasance abin kyama, abin kyama ne." 

Wakilai daga kasashe 19 da suka hada da Faransa da Jamus da Japan da Birtaniya sun ziyarci Huwara ranar asabar da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.