Isa ga babban shafi

Gwamnati ta karrama limamin da ya tausasa kyanwa a Salla

Gwamnatin Algeria ta karrama limamin nan, Imam Walid Mehsas wanda kyanwa ta dare jinkinsa a daidai lokacin da yake jagorantar Sallar Taraweeh, inda cikin tausasawa ya yi ta shafar kwanyar wadda ta sunbace shi kafin daga bisani ta sauka daga jikinsa don ratsin kanta.

Imam Walid tare da Ministan Kula da Lamurran Addini na Kasar Algeria.
Imam Walid tare da Ministan Kula da Lamurran Addini na Kasar Algeria. © lechodalgerie.dz/wakfs
Talla

Wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta ne ya nuna yadda Imam Walid ya mu’amalanci kwanyar cikin kyawun yanayi, lamarin da ya kayatar da jama’a da dama hatta wadanda ba Musulmai ba daga sassan duniya.

Limamin ya sha yabo da jinjina, yayin da manyan kafafen yada labarai na duniya suka yi ta yada wannan labarin.

Yanzu haka gwamnatin Algeria ta gayyace shi tare da shirya masa taron liyafa na musamman, inda Ministan Kula da Lamurran Addini na Kasar, Dr. Youssaf Belmahdi ya yaba masa kan wannan kyakkyawar dabi’ar da ya nuna wa dabba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.