Isa ga babban shafi

Kasashen Larabawa na shirin maido da hulda da Syria

Kasar Qatar ta sanar da cewar kasashe 9 na Larabawa za su gudanar da wani taro a cikin wannan mako domin tattauna alakarsu da Syria da zummar kawo karshen wariyar da ake nuna mata sakamakon yakin basasar da ya mamaye kasar. 

Shugaban Syria Bashar al-Assad
Shugaban Syria Bashar al-Assad © REUTERS/SANA
Talla

Ma’aikatar Harkokin Wajen Qatar ta ce taron wanda zai gudana a Saudi Arabia a wannan Juma’ar zai kunshi kasashe irin su Bahrain da Kuwait da Oman da Qatar da da Saudi Arabia da kuma Daular Larabawa. 

Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar Majed Al-Ansari ya ce sauran kasashen da ake sa ran su halarci taron sun hada da Masar da Iraqi da Jordan, yayin da batun Syria shi ne zai mamaye abin da ministocin kasashen za su mayar da hankali a kai. 

Shugaban Syria Bashar al Assad da aka mayar da shi saniyar ware tun bayan barkewar yakin basasar kasarsa a shekarar 2011, ya ziyarci Daular Larabawa da kuma Oman a watanni 2 da suka gabata, inda ya tattauna da shugabannin kasashen. 

Kasar Saudi Arabia a watan jiya ta sanar da cewar ta fara tattaunawa da shugabannin Syria da zummar ganin sun koma gudanar da harkokin diflomasiya a tsakanin kasashen biyu. 

Kungiyar Kasashen Larabawa ta kori Syria daga cikinta sakamakon yakin da aka samu a kasar da kuma zargin murkushe masu zanga-zangar dimokiradiya. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.