Isa ga babban shafi

Ba za mu lamunci mayar da kasashen Larabawa filin yaki ba - Saudiyya

Yarima mai jiran gado na Saudiyya, kuma firaministan kasar, Mohammed bin Salman, ya jaddada kudurin kasashen Larabawa na kawo karshen duk wani yaki da ke addabar yankin Gabas ta Tsakiya.

Yariman Saudiyya Mohammed Bin Salman, lokacin da yake maraba ga shugaban Syria Bashar al-Assad a Saudiyya.
Yariman Saudiyya Mohammed Bin Salman, lokacin da yake maraba ga shugaban Syria Bashar al-Assad a Saudiyya. AP
Talla

“Muna tabbatar wa da kasashen kawance a gabashi da yamma cewa za mu samar da zaman lafiya mai dorewa. Ba za mu bar yankinmu ya koma wani filin yaki ba,” in ji yarima mai jiran gado yayin bude taron kungiyar kasashen Larabawa karo na 32.

“Yankin Larabawa ya gaji da rigingimu. “Ya ishe mu, mu tuna shekaru masu tsauri saboda rikice-rikicen da yankin ya rayu a ciki. Mun gaji da rigingimun da al’ummar yankin mu suka sha fama da su, wanda a dalilin haka ne ci gaban kasashen mu suka tabarbare,” inji Yarima Salman.

Yarima Mohammed ya bayyana irin karfin da kasashen Larabawa ke da shi, inda ya ce kasashen suna da karfin al'adu da albarkatun kasa da za su iya amfani da su wajen samar da ci gaba a dukkan fannoni.

Yarima mai jiran gadon sarautar Saudiyya, ya yi maraba da shugaban Syria Al-Assad da ya koma cikin kasashen Larabawa, yana mai cewa: "Muna fatan komawar Syria cikin kungiyar kasashen Larabawa zai kawo karshen rikicinta."

Al-Assad na halartar taron a karon farko cikin shekaru 12, sai kuma shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky da ya kasance babban bako a taron.

Yarima Mohammed bin Salman ya jaddada cewa batun Falasdinu shi ne kuma har yanzu babban abin da suke kokarin kawo karshen sa.

Mohammed bin Salman ya jaddada muhimmancin warware rikicin Ukraine cikin lumana.

Taron na yini guda dai ya fi mayar da hankali ne kan batun komawar Syria cikin kungiyar kasashen Larabawa da kuma halin da ake ciki a Sudan da kuma batun Falasdinu.

Taron na kasashen Larabawa ya hada kasashe mambobi 22 da shugabannin kasashe da gwamnatocin kasashe 22 ke wakilta tare da kasashe biyar masu sa ido.

Saudiyya ce ke karbar bakuncin taron bayan karbar ragamar shugabancin kungiyar daga Aljeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.