Isa ga babban shafi

Taliban ta zartar da hukuncin kisa a cikin Masallaci

A wannan Talata, gwamnatin Taliban a Afghanistan ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar bindigewa bainar jama’a, wanda shi ne karo na biyu da ake zartar da irin wannan hukunci tun lokacin da kungiyar ta karbi ragamar mulki a 2021. 

A karo na biyu kenan da Taliban ke aiwatar da irin wannan hukuncin kisan a bainaar jama'a domin gargadin jama'a.
A karo na biyu kenan da Taliban ke aiwatar da irin wannan hukuncin kisan a bainaar jama'a domin gargadin jama'a. Associated Press - KAMRAN JEBREILI
Talla

An zartar da hukuncin kisan ne ta hanyar bindigewa a wani gari mai suna Sultan Ghazi Baba da ke lardin Lagman a tsakiyar kasar, kuma a cewar mahukuntan Taliban, an zartar da hukuncin bainar jama’a ne domin ya kasance gargadi ga sauran masu aikata laifufuka. 

Kafin zartar da hukuncin a cikin masallaci, sai da aka bayyana sunan mai laifin a matsayin Ajmal dan Naseem,  kuma an same shi da laifin kisan mutane biyar ne, saboda haka aka aiwatar da hukuncin a gaban mutane sama da dubu biyu. 

Aiwatar da hukuncin kisa a lokacin da kungiyar Taliban ta mulkin Afghanistan tsakanin 1996 zuwa 2001 ya kasance ruwan dare, amma daga lokacin da ta sake dawowa kan madafan iko, wannan ne karo na biyu da hakan ta faru. 

To amma duk da cewa ba kasafai sabuwar gwamnatin Taliban ke aiwatar da kisa a kan wadanda aka sama da laifi ba, amma sau da dama ana yin bulala ga wadannan suka aikata wasu laifufuka, da suka hada da sata, zina da kuma shan barasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.