Dubban mutane sun yi zanga-zangar kin jinin Isra'ila a sassan duniya
Dubban mutane sun bazama kan tituna a sassan duniya musamman a kasashen yankin Gabas ta Tsakiya, domin nuna goyon bayansu ga Falasdinawa, a daidai lokacin da Isra'ila ke shirin kaddamar da farmaki ta kasa kan Zirin Gaza.
Wallafawa ranar:
Masu zanga-zangar sun yi ta yin tir da harin bama-bamai ta sama da Isra’ila ke kai wa kan yankin na Gaza babu kakkautawa, inda ya zuwa yanzu sama da mutane dubu 1 da 900 suka mutu, matakin da ta ce martani ne kan farmakin ba-zatar da mayakan Hamas suka kaddamar kanta, tare da kashe mata mutane fiye da 1 da 300.
A Bagadaza babban birnin kasar Iraqi, dandalin taro na Tahrir jama'a suka cika domin amsa kiran jagoran mabiya Shi'a Muqtada al-Sadr don yin Allah wadai da Isra’ila.
A Sanaa kuwa, babban birnin Yemen da kuma kasar Jordan, masu zanga-zangar da suka fita kan tituna, daga tutocin kasashen suka rika yi da na Falasdinawa.
A birnin Islamabad na Pakistan, taka tutocin Amurka da na Isra’ila masu zanga-zanga suka rika yi gami da yin Alla wadai da su.
A Kuala Lumpur babban birnin kasar Malaysia, kimanin Musulmai dubu 1 ne suka gudanar da zanga-zanga tare da kona tutocin Isra'ila.
Malaman addinin Musulunci a Indonesia kuwa, kira suka yi ga dukkanin masallatan kasar da su gudanar da addu’o’i na musamman don nemawa Falasdinawa tsaro da zaman lafiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu