Isa ga babban shafi
SUDAN

Shugaba Omar al-Bashir Yayi Jawabin Amincewa da Zaben Raba Gardama

Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir yayi jawabin neman zaman lafiya ga alummar kasar yau. Shugaban yayi jawabin nashi ne a yankin Juba dake kudancin kasar inda yayi fatan ganin anyi zaben raba gardama mai zuwa lami lafiya.A kalla mutane kusan miliyan hudu sukayi rajistar kada kuri’u, a zaben raba gardamar da za’ayi a kudancin Sudan, abinda ake ganin zai haifar da raba kasar biyu.Mataimakin shugaban Hukumar zaben kasar, Chan Reec, yace kashi 51 na wadanda sukayi rajista, mata ne, kuma daga yau talata, za’a akai takardun kada kuri’u kowanne sako.A halin da ake ciki Kasar Sudan tace a shirye take ta amince da sakamakon zaben raba gardaman, muddin  an gudanar dashi bisa ka'ida.Minstan harkokin waje na kasar Ali Karti ne ya bayyana haka inda yake cewa.

Shugaba Omar al-Bashir  na kasar  Sudán
Shugaba Omar al-Bashir na kasar Sudán rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.