Taron Shugabannin Kasashen Africa Na Duba Lamarin Kasar Libya
Kotun duniya mai hukumta laifukan yaki dake birnin La Haye CPI ta bada sammacin kamo mata shugaban kasar Libiya Canal Ma’amar Khadafi, da dansa Saiful al-Islam, da kuma shugaban hukumar leken asirin kasar Abdallah Al Senoussi, bisa tuhumarsu da laifukan yaki da cin zarafin bil’adama.Matakin mika sammacin da alkalin kotun ta duniya ya dauka, ya haifar da murna a birnin Beghazi, birnin na biyu a kasar, da kuma birnin Misrata mai tazarar kilo mita 200 gabashin Tripoli babban birnin kasar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Yayin da rikicin kasar Libya ke cikin abubuwan da shugabannin Afrika zasu tattauna akai, yanzu sammacin kamo shugaba Muammar Gaddafi ya janyo lamarin ya dauki sabon salo.
Suleiman Babayo daga Malabo babban birnin kasar Equatorial Guinea ya aiko mana da rohoto akai:
Rahoton Sulaiman Babayo
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu