Isa ga babban shafi
Lafiya Jari ce

Cutar Ido Ta Glacouma

Wallafawa ranar:

Alkalumma daga hukumar lafiya ta duniya WHO,sun nuna cewa cutar ido ta Glaucoma dake farawa da dushewar ido ko gani biji-biji,na shafar akalla mutane miliyan 2 a doron-kasa kowacce shekara,inda kuma kashi 75 cikin 100 na wannan adaddin ke makancewa. Wannan inji hukumar ta WHO,yasa cutar ta Glacouma,cikin cututtuka mafi hadari dake shafar ijiya ko idon dan Adam a duniya.Kamar yadda bincike ya nuna,wani abinda ke cigaba da daurewa masana da kwararru kai game da cutar ta Glacouma,shine duk da hadarin dake tattare da wannan cutar ga idon dan Adam,tantance ta cikin lokaci kuma da wuri kafin tayi illa,nada wuyar gaske. Binciken ya nuna cewa ba wai karancin likitoci ko magungunan tunkarar cutar ke da wuya ba,illa dai kawai matsalar tantance ta cikin lokaci.Shirin Lafiya-Jari na wannan makon,ya duba illa wannan cutar ta Glacouma,wasu daga cikin dalilan dake haddasa ta da kuma kalubalen tunkarar ta daga bangaren masana da hukumomi.

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.