Isa ga babban shafi
Lafiya

An kaddamar da gagarumin aikin kawar da Malaria a Afrika

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, yanzu haka an kaddamar da wani gagarumin aikin rigakafin cutar Malaria a Afrika domin kawo karshen yadda cutar ke ci gaba da yiwa jama’a illa.

Akalla mutane miliyan 4 ke kamuwa da cutar Malaria kowacce shekara wadda ke kai ga mutuwar tsakanin mutane dubu 21 zuwa dubu 143.
Akalla mutane miliyan 4 ke kamuwa da cutar Malaria kowacce shekara wadda ke kai ga mutuwar tsakanin mutane dubu 21 zuwa dubu 143. REUTERS/James Gathany
Talla

Shirin aikin da ake saran mutane miliyan biyu za su amfana da shi, zai shafi kasashen Malawi da Najeriya da Sudan ta Kudu da Uganda da kuma Zambia.

Shugaban Kungiyar Agaji ta Gavi da ke hadin kai da Majalisar Dinkin Duniya wajen gudanar da aikin, Seth Berkley ya ce, wannan shi ne shiri mafi girma da aka taba yi kan cutar ta zazzabin cizon sauro.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, akalla mutane miliyan 4 ke kamuwa da cutar kowacce shekara wadda ke kai ga mutuwar tsakanin mutane dubu 21 zuwa dubu 143.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.