Isa ga babban shafi

Mutum 730,000 ke kashe kansu duk shekara - WHO

Hukumar Lafiya ta duniya WHO, tace a kowacce shekara mutane dubu 730 ke kashe kansu da kansu, sakamakon wasu matsalolin rayuwar da suka addabe su, abinda ke nuna cewar a cikin kowacce dakika 45 mutum guda na kashe kansa a duniya.

fasalin igiyar da ake rataye masu laifin da hukuncin kisa ya hau kansu.
fasalin igiyar da ake rataye masu laifin da hukuncin kisa ya hau kansu. © REUTERS
Talla

Sanarwar da Hukumar ta gabatar sakamakon bikin ranar yaki da kisan kai na wannan shekaran yace, duk lokacin da wani ya kashe kansa, akwai wasu mutane 25 da suka yi irin wannan yunkuri ba tare da samun nasara ba.

Hukumar tace kashe kai shine hanya ta 4 na rasuwar da ake samu tsakanin matasa masu shekaru tsakanin 15 zuwa 19, kamar yadda binciken da aka gudanar ya nuna a kasashe masu tasowa.

Rahotan ya nuna cewar a shekarar 2019, mutane sama da dubu 700 suka kashe kansu da kansu, kuma a kowanne mutuwar mutane 100 da ake samu, guda kisan kai ne, amma lamarin kan sauya tsakanin kasa zuwa kasa, da kuma tsakanin maza da mata.

Hukumar tace an fi samun adadin mazan dake kashe kansu akan mata a kasashen da suka ci gaba, yayin da mata sun fi kashe kansu a kasashe masu tasowa.

Alkaluman Hukumar sun nuna cewar Afirka itace gaba a matakin farko da sama da kashi 11 na mutanen dake kashe kansu, sai nahiyar Turai mai kashi 10 da rabi, yayin da Gabashin Asia ke da sama da kasha 10.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.